Mal. Umar Ahmad Ali
 ya bayyanawa manema labarai makasudin wannan taro na yaye É—alibai  Mata 56 Maza 50, kuma yayi kira ga matasan kan kokarin aiki da umartuwa da alqur'ani maigirma, sannan ya bayyan irin matsalar da makarantar ke fuskanta na rashin matsugunni da masu hannu da ahuni da ita kanta gwamnati tayi burus domin sama musu. Shima Sakataren wannan makaranta
 Mal. Muhammad Dayyib (Mal.wada) 
yaja hankalin na wandannan matasa da kada su dakata da neman ilimi ganin sun sauke face su É—ora wata É—anba ta karo karatu a kan sanin alqur'ani Maigirma.  Shima shugaban kwamitin iyaye na wannan makaranta 
Mal. Shu'aibu Mustapha Umar 
yaja hankali da su ɗora da cigaba da neman ilimi kuma iyaye su ƙara ƙoƙari a kan baiwa yaran su gudunmawa wajen neman ilimi domin girbar mai jyau ranar tashin alkiyama.
