Duk da cewa daraktan yada labarai da ka’idojin shari’a na jihar, Abbas Rufa’i, bai fayyace irin laifin da alkalin ya aikata ba, amma jaridar Raihana ta jiyo cewa an tuhume shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu bayan da mai kara ya shigar da kara a gabansa kan karbar N50,000 cin hanci a hannun sa.
“Hukumar ta yanke hukunci na hadin kai kan yin ritayar dole ga Alkali Safiyanu Muhammad bisa laifin da ya aikata a lokacin da wani mai kara ya gurfana a gabansa a wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Birnin Kudu,” in ji Mista Rufa’i a wata sanarwa a yau Asabar.
Sai dai hukumar ta gargadi ma’aikatan ta da su guji duk wani nau’i na cin hanci da rashawa domin a tsaftace bangaren shari’a a jihar.
Don haka ta kara da cewa hukumar ta sake jaddada aniyar ta na tunkarar duk wani ma’aikaci da aka samu da cin-hanci to zai ɗanɗana kuɗarsa.