Shugaban cocin Cathedral Presbyter and Administrator, Methodist Cathedral Church, Aba, Very Rev Henry Anozie, ya ce kamata ya yi gwamnati ta yi amfani da lamunin tallafi na bankin duniya na kwanan da za ta karɓo don gyara matatun mai maimakon raba kuɗin ga ƴan ƙasa.
Anozie, wanda ya yi magana da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya a Aba, Abia, ya ce gyara matatun man zai haifar da tasirin tattalin arziki da zai inganta tattalin arzikin iyali fiye da raba kuɗin.
Ya kara da cewa tun da sufuri ke sarrafa yawancin ayyukan tattalin arziki a Najeriya, farfado da matatun man da rage tsadar man fetur zai fi taimakawa gidaje fiye da “raba musu kudi”.
Mista Anozie ya ce raba kudin ga wasu gidaje ba zai rage radadin talauci ba kamaryadda amfani da rancen kuɗin wajen gyaran matatun mai zai yi.
“Ya bayyana cewa idan mutanenmu suka shiga mukaman shugabanci, shaidan yakan juyar da kwakwalwarsu.
“Idan ka ci gaba da baiwa mutane kudi su je su ci ba tare da sun yi aiki ba, nan ba da dadewa ba kudin zai kare kuma mutum zai ci gaba da zama haka ya koma bara.
“Ina ganin shirin raba kudin ba zai taimaka sosai ba. Babban fifiko ne mara kyau.
“Ya kamata gwamnati ta sake gyara matatun man da kudin, ta sa mutane su yi sana’o’i masu ma’ana da za su yi tasiri ga tattalin arzikinmu.