Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Olisa Ifeajika, ya musanta zargin korar a wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi a Asaba. Jaridar Raihana ta rawaito cewa
Ya bayyana cewa, Ogochukwu Nwabude mai shekaru 32, waccw a kodayaushe ta ke rike da jariri, na zama a shatale-talen Inter Bau da ke kan titin Asaba-Okpanam, kimanin makonni biyu ta na bara.
A cewar Ifeajika, jami’an ma’aikatar harkokin mata da ci gaban jama’a ta jihar sun gudanar da bincike na sirri a kan matar.
“Bayan an lura da ita na wani lokaci, an bayyana cewa tana cikin kwanciyar hankali kuma tana da cikakken hankali, kawai dai tana buƙatar taimakon kuɗi ne.
“Damuwa da halin da matar ke ciki, kuma kamar yadda tsarin karɓar irin waɗannan lamura ya ke, ma’aikatar ta ba ta wasu taimako, musamman da take tare da jariri.
“Bayan haka, ta mayar da ita ga takwararta ta ma’aikatar harkokin mata da ci gaban jama’a a Anambra don samun tallafin da ya dace,” in ji shi.