Bayan karɓar rantsuwa a ranar 29 da watan Mayun da ya gabata, zaɓaɓɓen gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya kafa kwamitin kar ta kwana domin kawo Rahoton abubuwan da ake bukata a ma'aikatar samar da ruwan sha ta jihar Kano, wacce gwamnan Kano ya ce basu tarar da kayan aikin da za'a iya tura ruwa zuwa yankunan jihar ba.
A yanzu dai a iya cewa al'ummar jihar Kano sun kusa darawa, domin sabon shugaban hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano, Injiniya Garba Bichi, ya tabbatar da cewa, ya fara karɓar kayayyakin aiki don tura ruwa ga al'umma, wanda aka kawo Alumun daga gwamnati a matatar ruwa ta Chalawa Dake Karamar Hukumar Kumbotso.