Hassan Ogbole, mataimakin darakta mai sa ido da bibiya na sashen kula da ci gaba na babban birnin tarayya Abuja, shi ne ya bayyana hakan a ci gaba da aikin tsaftace muhalli a Gishiri a yau Juma’a.
Ya ce haramtattun gine-gine da sauran ayyukan da ake yi a yankin sun shafi babban tsarin Abuja don haka dole ne a rusa su domin dawo da su hayyacin su.
“Wannan shi ne karo na uku da za mu ziyarci Gishiri a ci gaba da tsaftace birnin domin dawo da babban tsarin Abuja na ainihi.
“Mun damu da kwato filaye da wasu mutane suka karbe ba bisa ka’ida ba don dalilai daban-daban, domin dawo datsarin Abuja na ainihi.
Ogbole ya yi kira ga masu filaye e halastattu da su fara aikin gini cikin gaggawa domin hana dawowar haramtattun gine-gine.
“Wadanda ke da rabon filayen ya kamata su dauke su cikin gaggawa don gujewa sabbin abubuwan da suka sabawa doka, su bar masu su shigo su fara aiki a ciki” in ji shi.
