Ginin mai hawa huÉ—u ya rufta kan wani ginin da misalin karfe 1:00 na safe agogon GMT a arewacin birnin, kamar yadda wani babban jami'in hukumar kashe gobara ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Ɗan majalisar karamar hukumar Douala,Charles Elie Zang Zang, ya ce jami'an ceto na neman waɗanda suka tsira daga ɓaraguzan ginin.
Asibitin Laquintinie da ke Douala ya ce an kai masa waÉ—anda suka jikkata su 13 kuma ya ce biyu daga cikinsu - da suka haÉ—a da yarinya 'yar shekara uku da budurwa 'yar shekara 19 - sun mutu.
Ya kara da cewa wasu yara uku na karɓar kulawar gaggawa.