Bokan da aka fi sani da Akwa Okuko Tiwaraki, na nufin ‘kwai mai karya kwaran manja’ a turance.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kashe mataimakansa guda biyu a lokacin da aka yi garkuwa da shi a daren Lahadi.
Wata majiya ta ce mutumin wanda ake kyautata zaton yana ɗaya daga cikin bokaye mafiya karfi a jihar ta Anambra, an yi garkuwa da shi cikin sauki a otal ɗin sa mai suna Triple P Hotel, tare da bindige wasu mukarraban sa guda biyu har lahira.
Ana kuma kallon Akwa Okuko Tiwaraki a matsayin mai maganin gargajiya mafi kuɗi a jihar.
A 2022 ya gina tare da ƙaddamar da otal guda biyu, waɗanda aka ɗauka a matsayin mafi girma a Oba.
Majiyoyi, sun ce sace shi ya janyo ce-ce-ku-ce da kuma raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa yana ɗaya daga cikin bokaye mafiya karfi.
Hukumomin ƴan sanda a jihar sun tabbatar da faruwar lamarin, inda ma magana da yawunsu, DSP Toochukwu Ikenga ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na dare, sai dai daga bisani an sako bokan da aka sace.