Manyan Majiyoyi Sun Bayyana Cewa Tsohon Gwamna Umar Ganduje Yana Samun Goyon Bayan Manyan Jigogin Jam'iyyar APC Na Zama Shugaban Jam'iyyar APC Na Kasa.
Muƙamin ya tabbata ne bayan da manyan masu faɗa aji na jam'iyyar sukai tattaunawa ta musamman wanda a ƙarshe aka tsaida matsaya kan a baiwa tsohon gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje riƙon jam'iyyar sannan aka amince da Sen. Ajibola Basiru Matsayin sakataren jam'iyyar.