Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa da ke zamanta a Abuja ta jingine hukuncin da ta yanke a kan ƙorafin da Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na babbar jam'iyyar adawar Najeriya wato PDP ya shigar a kan zaɓen 25 ga watan Fabrairu.
Atiku yana ƙalubalantar nasarar Bola Tinubu a matsayin shugaban ƙasa a babban zaɓen ƙasar.
Masu bayar da amsa a ƙarar ta Atiku Abubakar su ne Hukumar Zaɓe ta INEC da Bola Ahmed Tinubu da kuma jam'iyyar APC mai mulki.
Kotun bayan ta karɓi rubutattun jawaban ƙarshe daga kowanne ɓangare, sai ta sanya hukuncin da ta yanke a mala wato ta jingine shi ya zuwa wata rana da za ta sanar da ɓangarorin da ke cikin shari'ar.
Hakan yana nufin hukunci kawai ya rage, kotun za ta sanar a wannan shari'a da jagoran adawar na Najeriya ya shigar.
Ranar 8 ga watan Mayun 2023 ne, kotun ta fara zama don sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen na shugaban ƙasa.