Rundunar Sojin Najeriya ta ce kiran da wasu 'yan ƙasar ke yi mata da ta yi juyin mulki "tsananin rashin kishin ƙasa ne da kuma mugunta".
Cikin wani saƙo da sojojin suka wallafa a shafinsu na Tuwita, sun ce suna mayar da martani ne sakamakon kiraye-kirayen da wasu ke yi suna fakewa da rashin kula da walwalar dakarunta.
"Hedikwatar tsaro ba ta jin daÉ—in kiraye-kirayen da ake yaÉ—awa a intanet game da walwalar dakarunta," in ji Birgediya Janar Tukur Gusau cikin wata sanarwa a ranar Juma'a.
"Yayin da muke ɗaukar walwalar dakarunmu da muhimmanci, muna kuma yin tir da yunƙurin wasu na neman Rundunar Sojin Najeriya mai bin doka ta sauya gwamnati a ƙasarmu ba ta hanyar da tsarin mulki ya tanada ba.
"Muna tabbatarwa ƙarara cewa rundunar ta gamsu kuma ta fi son zama a ƙarƙashin mulkin dimokuraɗiyya, kuma ba za ta yi wani abu da zai kawo wa dimokuraɗiyya cikas ba."
Juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar ya kasance na tara (har da yunƙurin da bai yi nasara ba) da aka yi a yankin Afirka ta Yamma tun daga 2020, inda ya shafi ƙasashen Mali, da Guinea, da Burkina, da Nijar - idan aka haɗa da Chadi.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, a matsayinsa na shugaban ƙungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma (Ecowas), shi ne ke jagorantar yunƙurin tilasta wa sojoji su mayar da Shugaba Bazoum Mohamed kan mulki da ƙarfin tsiya.