Sunanta Guichen Aghaichata ATTA, shekarunta 28, itace sabuwar ministar yawon bude ido da kasuwanci da sojojin kasar Nijar suka nada.
Aghaichata mace ce mai himma sosai wajen inganta dabi'un al'adu da kuma kokari don kawo cigaba ga matasa. Tana da digiri biyu a fannin kasuwanci da ta samu a kasar Maroko.