Kwamishinan na kano ya bada wannan sanarwar ne yayin ƙaddamar da wasan ƙwallo da sukai alƙawarin bugawa da tubabbun ƴandaba.
A wancan lokacin basu fi ƴandaba 20 wanda kwamishinan ya sanar da neman su ba, amma sai da hukumar ta samu tubabbu da suka kawo kansu kimanin 90 da ɗoriya wanda suka kawo kansu suka ajiye makamai, kuma kwamishinan y shirya musu wasan ƙwallo dlwanda suka fara buga yau a filin ƙwallo na SANI ABACHA dake ƙofar mata a garin kano.
Sai dai an tsumayi ajiye makaman wasu manyan ƴandaba da suka kai guda uku amma basu kawo kansu ba kuma ba'aji ɗuriyar su ba, hakan ce tasa kwamishinan ƴansandan ya sanar dasu a matsayin WANTED wato ana neman su ruwa a jallo tare da alƙawarin baiwa duk wanda ya kawo su nera dubu ɗari 100,000, loda kuwa sun kai sama da ɗaya za'a baiwa kowanne nera dubu 100,000. Waɗanda ake nema ruwa a jallo sun haɗar da: Burakita daga Ɗorayi qtrs, Hantar Daba daga Tudun Fulani Unguwar ɗisu da kuma Chila Mai Doki daga Unguwar Tudun Fulani.