A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter, ma'aikatar harkokin wajen Faransa, ta ƙara nanata adawa da juyin mulki a Nijar da kuma tsare Shugaba Bazoum.
Ita ma Amurka ta bakin Sakataren Wajenta, Anthony Blinken, ta ce "Gwamnatin Washington na goyon bayan duk wani mataki da Ecowas za ta ɗauka don ganin an dawo da tsarin dimokraɗiyya Nijar".
Ta kuma ce za ta ɗora alhakin duk abin da ya faru ga lafiyar Bazoum da kuma iyalansa a kan sojojin.
Nijar, na ɗaya daga cikin ƙasashe mafi talauci a duniya, kuma ba ta kusa da teku. Girmanta ya kai misalin faɗin Faransa biyu, ita ce ƙasa ta bakwai a duniya da ke samar da makamashin uranium, wani muhimmin sinadari da ake amfani da shi wajen sarrafa makamashin nukiliya da kuma haɗa magungunan cutar daji ko kansa.
Kafin juyin mulkin, Nijar ta kasance abokiyar ƙawance ga Ƙasashen Yamma, amma yanzu ta juya wa uwargijiyarta Faransa baya inda take yunƙurin ƙulla alaƙa da Rasha.
Akwai dakarun Amurka da Faransa da Jamus da kuma na Italiya a Nijar, a matsayin wani ɓangare na yaƙi da masu iƙirarin jihadi da ya bazu a faɗin yanki Sahel.