Ranar Asabar 17 ga watan Mayu ne aka yi bikin kaddamar da littafin Sirrin Mace Musulma, wanda matashiyar marubuciya Fatima Aminu Alhassan Kabo.
Taron, wanda aka gabatar a kofar gidan hakimin Kabo, ya samu hakartar shugaban karamar hukumar Kabo Hon. Lawal Najume Kano, wanda shi ne babban mai kaddamarwa, tare da manyan 'yan siyasa da suka fito daga wannan karamar hukuma, wadanda suka hada da wakilan Barau Jibrin, Nasiru Sulen Garo daMurtala Sulen Garo, sai masu sarauta da sauran jama'ar gari.
Littafi ne dai da aka rubuta shi a kan abin da ya shafi addini musamman don amfanin 'ya'ya mata wajen kula da ibada da tarbiyyarsu.
A nasa jawabin, babban baƙo mai jawabi, Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino MON, Sarkin Mawallafan Arewa,ya yaba wa marubuciyar bisa kokarinta. Sannan ya yi kira ga al'ummar garin su daure su sayi littafin don amfanuwar su. Haka nan ya yi kira ga 'yan siyasar garin da ma na jiha baki daya da su dauki nauyin wallafa littafin da yawa don rabawa ga makarantu don karuwarsu da ilimin da ke cikin littadin.
Sauran manyan baƙi sun jaɗa da Wadanda suka halarta
1. Alhaji Lawan Najume
Kabo LGA chairman
2. Wakilin DSP Senator
Barau I Jibrin
Deputy senate president, Wakilin Hakimin Kabo
Alh. Idris Adamu Dankabo
4. Wakilin Hon Nasiru Sule Garo
Commissioner of special Duty
5. Wakilan Alhaji Fahad Adamu Dankabo
Daga bangaren marubuta kuma taron ya samu halartar Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino MON, Sarkin Mawallafan Arewa tare da Sakataren kungiyar marubuta ta kasa (ANA) reshen jihar Kano Ibrahim Muhammad Indabawa, da Malam Kabiru Yusuf Fagge (Anka) da kuma Malama Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo.