Gwamnatin Jihar Kano ta ja hankalin Al’umma da su tabbatar da Lafiyar Dabbobinsu na Layya gabanin Babbar Sallah
Gwamnatin Jihar Kano ta shawarci Al’umma da su tabbatar da duk dabbar da zasu yi layya da ita ba ta dauke da wata cuta
Sanarwar ta fito ne daga Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta bakin Kwamishinan Lafiya na Jihar Dr. Abubakar Labaran Yusuf domin kare lafiyar jama’a da kuma dakile yaduwar cututtuka da dabbobi ke iya haddasawa ga Al’umma.
Kwamishinan ya kara da cewa wajibi ne jama’a su kula da lafiyar dabbobin da za su siya domin layya.,inda yace akwai wasu dabbobi da suke dauke da wasu cututtuka da za su iya yadawa ga jama'a, musamman idan ba a kiyaye matakan kariya ba wajen yanka da kuma dafawa ba.
Dakta Yusuf ya kuma yi kira musamman ga iyaye mata da masu dafa abinci da su tabbatar da cewa sun wanke naman da ruwa mai tsafta,da kuma dafa naman sosai,wanda hakan zai taimaka matuka wajen kashe kwayoyin cuta da ke iya kasancewa a jikin naman.
Dakta Labaran ya kara da cewa Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Mai Girma Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ta tanadi isassun magunguna da kayan agajin gaggawa a asibitocin gwamnati, domin bayar da taimakon gaggawa idan buƙatar hakan ta taso.
Hakazalika Kwamishinan ya kuma bayyana cewa Ma’aikatar Lafiya ta jihar kano za ta ci gaba da wayar da kan Al’umma kan matakan kariya da lafiyar jama’a, musamman a irin wannan lokaci na bukukuwa da ta’ammali da nama ke karuwa, lamarin da ke kara barazanar yaduwar cututtuka ga jama'a.
A karshe, Dakta Yusuf ya yi fatan al’ummar Jihar Kano za su gudanar da bukukuwan Sallah cikin kwanciyar hankali, lafiya, da farin ciki.