Kasar Saudiyya ta amince da bukatar binne Marigayi Aminu Dantata a Madina
Gwamnatin Saudiyya ta amince a yi jana’iza tare da binne gawar attajirin É—an kasuwar nan na Kano, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, a Æ™asar.
Babban sakataren marigayin, Mustapha Abdullahi Junaid ya ce shirye-shirye sun kammala domin gudanar da jana’iza tare da binne gawar marigayin a garin Madina.
Makosancin Marigayi mai suna Mustapha ne ya tabbatar da hakan inda yace “Alhamdulillah an samu amincewar (hukumomi).
“Za a É—auki Aminu Alhassan ÆŠantata daga Abu Dhabi zuwa birnin Madina.
Za kuma a yi jana’izarsa a ranar Litinin da safe in sha Allah.” a cewar sa.
A ranar Asabar ne shahararren É—ankasuwa Aminu ÆŠantata ya rasu yana da shekara 94 da haihuwa a shekarar miladiyya.
A shekarar Hijira (ta Musulunci) kuma, ya rasu yana da shekara 97, kamar yadda sakatarensa Mustapha Abdullahi ya bayyana.
Hamshaƙin attajirin ya rasu ne a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa bayan fama da jinya, kamar yadda wani ɗansa ya bayyana.
Bayanai sun nuna cewa marigayin ya sha bayyana sha’awarsa cewa “Allah ka kashe ni a wannan gari” a duk lokacin da ya ziyarci garin Madina da ke Saudiyya.
Wannan karon farko a tarihi da aka yi shgar da gawar wani da dana dan kasar ba zuwa Saudiyya a kuma binne a can.