Matatar Dangote za ta rarrarba Man Fetur kai-tsaye zuwa gidajen Mai
Matatar Dangote ta sanar da cewa zata fara rarraba man fetur (PMS) da dizal a duk faÉ—in Nijeriya tun daga ranar 15 ga Agusta, 2025.
Wannan shiri zai baiwa masu sayarwa, da ‘yan kasuwa, da masana’antu da sauran manyan masu amfani damar sayen Man kai tsaye daga kamfanin.
Don inganta hanyoyin rarrabawar Matatar ta ƙaddamar da sabbin tankokin iskar gas (CNG) guda 4,000 da kuma gina tashoshin samar da iskar ta CNG.
Wannan tsarin zai rage farashin sufuri da kuma taimakawa wajen rage farashin kayayyaki masu amfani da man fetur.
Sanarwar ta nuna cewa wannan shiri ya yi daidai da shirin “Renewed Hope Agenda” na Shugaba Bola Tinubu. An buÆ™aci masu sha’awar shiga wannan shirin su yi rijista tsakanin ranar 16 ga Yuni zuwa 15 ga Agusta.
Matatar ta ce, wannan shiri na daga cikin Æ™oÆ™arinsa na taimakawa wajen samar da man fetur mai arha a Nijeriya, wanda zai inganta rayuwar al’umma da tattalin arzikin kasar.