Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya sanya hannu kan dokokin gyaran haraji guda huɗu da suka samu amincewar majalisun dokoki na tarayya, a wani mataki da ake ganin zai sauya tsarin haraji da tattalin arzikin ƙasar gaba ɗaya.
Bikin sanya hannun ya samu halartar shugaban majalisar dattawa, kakakin majalisar wakilai, shugabannin kwamitocin kudi na majalisu, shugaban kungiyar gwamnoni, ministan kudi da kuma babban lauya na ƙasa.
Dokokin da aka sanyawa hannu sun haÉ—a da Kudurin Dokar Haraji na Najeriya, Kudurin Dokar Gudanar da Haraji, Kudurin Kafa Hukumar Tara Haraji ta Najeriya, da Kudurin Kafa Hukumar HaÉ—in Gwiwar Tara Haraji.