Wannan na cikin wata sanarwa da mai taimakawa Ministan Yaɗa Labarai, Rabiu Ibrahim, ya fitar a Litinin, 30 ga Yuni, 2025.
Sanarwar ta ce Ministan Tsaro kuma tsohon Gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ne ke jagorantar tawagar, tare da Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Ƙasa, Prince Lateef Fagbemi (SAN), Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris da Karamin Ministan Gidaje, Yusuf Abdullahi Ata.
Sauran da ke cikin tawagar sun haɗa da Dr. Bashir Aliyu Umar, Sheikh Aminu Daurawa da Khalifa Abdullahi Muhammad — limamin masallacin Dantata da ke Abuja, tare da wakilan ofishin jakadancin Najeriya a Jeddah ƙarƙashin jagorancin Ambasada Muazzam Ibrahim Nayaya.