Belin Dan Safarar Kwaya: Gwamna Kano Alh Abba K Yusuf Yya Umurci ai Bincike kan zargin hannun Kwamishinan Sufuri
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan zargin da ake yi wa Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Namadi, dangane da belin wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Dan Wawu.
Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne bayan da aka samu zazzafar martani daga al’umma, sakamakon rahotannin da ke nuna cewa an ga sunan kwamishinan a cikin takardun gwamnati da suka shafi sakin wanda ake zargin.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar.
Don fuskantar wannan batu, Gwamna Yusuf ya kafa wani kwamitin bincike na musamman karkashin jagorancin Mashawarcinsa na Musamman kan Harkokin Shari’a da Sabunta Kundin Tsarin Mulki, Barista Aminu Hussain. An dora wa kwamitin nauyin binciko gaskiyar lamarin da bayar da shawarwari kan matakin da ya kamata a dauka nan take.
Mambobin kwamitin sun hada da:
1. Barr. Aminu Hussain – Shugaba
2. Barr. Hamza Haladu – Mamba
3. Barr. Hamza Nuhu Dantani – Mamba
4. Alhaji Abdullahi Mahmoud Umar – Mamba
5. Manjo Janar Sani Muhammad (Mai ritaya) – Mamba
6. Kwamared Kabiru Said Dakata – Mamba
7. Hajiya Bilkisu Maimota – Sakatariya
Yayin da yake bayyana kafa kwamitin, Gwamna Yusuf ya nuna matukar damuwarsa kan wannan zargi na rashin gaskiya, inda ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi da kuma yaki da duk wasu munanan dabi’u a cikin al’umma.