Gwamnatin Taraiya ta karyata jita-jitar sakin ruwa daga Dam ɗin Lagdo na Kamaru
Gwamnatin tarayya ta musanta jita-jitar cewa an saki ruwa daga Dam ɗin Lagdo da ke ƙasar Kamaru zuwa Najeriya.
Akwai rahotanni da suka bayyana cewa ruwa daga dam ɗin an sako shi zuwa Najeriya, amma a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin, Ministan Albarkatun Ruwa da Tsabtace Muhalli, Joseph Utsev, ya ce bayan tattaunawarsa da Ahmad Bivoung, mai kula da dam ɗin, an bayyana masa cewa matakin ruwa a dam ɗin yanzu bai wuce mita 2.06 ba kuma babu wani ruwa da aka saki.
Utsev ya bayyana cewa ma’aikatarsa tana ci gaba da tattaunawa da hukumomin ƙasar Kamaru, kuma za ta sanar da ‘yan Najeriya nan take idan an saki ruwan.
“An shawarci jama’a da su yi watsi da waɗannan rahotannin ƙarya su kuma kwantar da hankula, tare da ci gaba da bin ka’idojin shirin kare kai daga ambaliyar ruwa da aka bayar a baya,” inji sanarwar.