Kungiyar lauyoyi ta Kano ta nemi Kwamishinan Sufuri ya bayyana mutanen da suka nemi ya yi belin wanda ake zargi kan miyagun kwayoyi
Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa reshen Kano ta bukaci Kwamishinan Sufuri na jihar da ya fito ya bayyana sunayen mutanen da suka shawarce shi ya tsaya wanda ake zargi da kasancewa mashahurin dillalin miyagun ƙwayoyi.
Wannan na cikin sanarwar da shugaban NBA reshen Kano, Usman Umar Fari, ya fitar a Jumu’ar nan 25 ga Yuli, 2025.
Sanarwar ta ce hujjar kwamishinan cewa ya tsaya ne bisa roÆ™on wasu manyan mutane ba abin gamsarwa ba ne ga al’umma, domin kuwa ya kamata a fayyace waÉ—anda suka nemi ya tsaya É—im.
NBA ta ce wajibi ne a bayyana ko mutanen suna cikin gwamnati ne, ko ’yan kasuwa ne ko kuma daga cikin masu rike da sarautun gargajiya.
Ƙungiyar ta ce idan har kwamishina a majalisar zartarwa zai tsaya wa wanda ake zargi da irin wannan babban laifi ba tare da sanin cikakken bayani ba, to hakan na nuni da rashin cancanta da kuma gazawa a matsayin da yake rike da shi.
NBA ta kuma buƙaci gwamnatin Kano ta bayyana matsayinta a hukumance kan lamarin, tare da buƙatar hukumomin tsaro su gayyaci kwamishinan domin ya bayyana sunayen waɗanda ke da hannu a lamarin, musamman idan akwai shakku game da rawar da suka taka a harkar safarar miyagun ƙwayoyi.
Daga ƙarshe, ƙungiyar ta shawarci gwamnati da ta rika zaɓar mutane nagari masu cikakken sani da amana wajen rike mukamai a gwamnatin jihar.