Tinubu ya tura Shettima a ɓoye ya ziyarci Buhari a asibiti a London
Shugaba Bola Tinubu ya tura mataimakinsa, Kashim Shettima, domin ya ziyarci tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a wani asibiti da ke London a ranar Litinin, kamar yadda wasu majiyoyi masu tushe su ka shaida.
Tsohon shugaban ya dade yana fama da rashin lafiya, kamar yadda Empowered Newswire ta fara rawaito wa, amma ana ganin yana samun sauƙi a halin yanzu.
Shettima ya kasance a Addis Ababa, Habasha, a gayyatar Firayim Minista Abiy Ahmed Ali domin halartar ƙaddamar da shirin Green Legacy Initiative (GLI) na ƙasar ta Gabashin Afirka.
Sai dai Tinubu — wanda ke wata ziyara ta ƙasa a St Lucia — ya umurci Shettima da ya tafi London domin duba tsohon shugaban ƙasar.
Shugaba Tinubu ya umarci Shettima da ya binciki yanayin lafiyar Buhari tare da tabbatar da an ba shi goyon baya har zuwa samun lafiya.
Shettima ya tashi daga Addis Ababa a daren Lahadi, inda ya isa London ranar Litinin kafin ya tafi wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba domin isar da saƙon Tinubu ga Buhari, in ji majiyoyin.
Stanley Nkwocha, mai magana da yawun Shettima, ya tabbatar da cewa shugabansa ya kai ziyara London amma ya ce ba zai iya cewa komai game da manufar ziyarar ba domin bai san cikakken jadawalin tafiyar ba.