A wannan rana ta Laraba 27-08-2025 Jihar Jigawa ta cika shekaru 34 da kafuwa
Yau Laraba wanda ta zo dai dai da 27 ga watan Agustan shekarar 2025, makwabaciyar Jihar Kano wato Jihar Jigawa ke cika shekaru 34 da kafuwa, a matsayin Jiha mai cin gashin kanta.
Hakan ta sanya wakilin Jaridar Raihana , Jameel Lawan Yakasai ya hada rahoto na musamman.
An kafa Jihar Jigawa daga tsohuwar Jihar Kano a ranar 27 ga Agusta, 1991, a zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
Don tunawa da wannan muhimmiyar rana, gwamnatin jihar ta ayyana yau Laraba a matsayin ranar hutu a duk fadin Jigawa, domin gudanar da shagulgula da bikin cika shekaru 34 da kafuwar jihar.
Jihar ta Jigawa na da kananan hukumomi guda 27, wadanda suka hadar da.
1. Auyo
2. Babura
3. Birniwa
4. Birnin Kudu
5. Buji
6. Dutse
7. Gagarawa
8. Garki
9. Gumel
10. Guri
11. Gwaram
12. Gwiwa
13. Hadeja
14. Jahun
15. Kafin Hausa
16. Kaugama
17. Kazaure
18. Kiri Kasamma
19. Kiyawa
20. Maigatari
21. Malam Madori
22. Miga
23. Ringim
24. Roni
25. Sule Tankarkar
26. Taura
27. Ƴan Kwashi
Jihar Jigawa daga kafuwar ta zuwa yanzu ta yi Gwamnoni guda 8, wadanda suka hadar da sojoji guda 3, fararan hula 5.
Sojoji sun hadar da.
1. Olayinka Sule 1991-1992
2. Ibrahim Aliyu 1993-1996
3. Rasheed Shekoni 1996-1998
Fararan hola 5
1. Ali Sa'ad Birnin Kudu 1992-1993
2. Ibrahim Saminu Turaki 1999-2007
3. Sule Lamido 2007-2015
4. Badaru Abubakar Talamiz 2015-2023
5. Umar Namadi 2023 har yanzu shike akan Mulki.
Kirarin da ake wa Jihar Jigawa shine "A Sabuwar Duniya" (The New World). Wannan kirarin yana nuna sabbin ci gaba da kuma cigaban da aka samu a Jihar Jigawa.