Daga Maryam Shehu Gadon Kaya
A ‘yan kwanakin nan, kafafen sada zumunta na zamani sun cika da labaran Æ™arya da zargi marasa tushe kan gaskiya, amana da nagartar wasu manyan jami’an siyasa na Gwamnatin Kano.
Ɗaya daga cikin irin wadannan labaran ƙarya da ake ganin an kitsa shi da gangan shi ne na jaridar Daily Nigerian, wata kafar labarai ta yanar gizo mai hedikwata a Kano,.
Jaridar ta wallafa wani labari a ranar 22 ga Agusta, 2025, inda ta zargi cewa an fitar da kuÉ—i daga baitul-mali na jihar Kano har naira biliyan 6.5 tare da karkatar da su.
Wannan zargi da ake yi, wanda a yanzu yana gaban kotu, akwai sunan Darakta Janar na Sashen Kula da al’amuran ofishin gwamna (Protocol Directorate) na Fadar Gwamnatin Kano, Alhaji Abdullahi Rogo.
Kan wannan ne ya sanya gwamnatin Kano ta magantu, inda ta bayyana matsayarta kamar haka.
1. Ba tare da an tsoma baki cikin shari’ar da ke gaban kotu ba, gwamnati na ganin wajibi ta fayyace wa jama’a yadda Sashen Kula da Bako ke gudanar da aikinsa a Fadar Gwamnatin Kano, wanda bai bambanta da tsarin da ake bi a sauran jihohi da kuma gwamnatin tarayya ba.
2. Da farko, gwamnati na jaddada cewa kowanne fitar kuÉ—i daga baitul-mali zuwa ga ma’aikatu, hukumomi da sassa na gwamnati (MDAs) ana yi ne bisa kasafi da aka tsara tare da lambobin lissafi da aka fayyace a tsarin kudi na shekara.
Saboda haka, babu wani mutum guda a cikin gwamnati da ke da ikon rike kuÉ—aÉ—en jama’a ba tare da takamaiman dalili da aka ware masa ba.
3. Sashen protocols na Fadar Gwamnatin Kano na da manyan ayyuka da suka haɗa da jigilar baki, masauki, walwala, da kuma tsara tafiyar Gwamna a cikin gida da wajen ƙasar nan.
4. Haka kuma, wannan sashi ne ke da alhakin samar da kayan aiki da bukatun jigila ga baki masu daraja kamar Shugaban Ƙasa, Ministoci, jami’an kasashen waje, da sauran baki na diflomasiyya da ke zuwa Kano a hukumance.
Wannan ya haÉ—a har da ‘yan Æ™asa na gari da Gwamna ke bai wa kulawa ta musamman.
5. Kusan kashi 95% na aikin wannan sashi ya ta’allaka ne da harkokin kuÉ—i masu yawa, wanda galibi ake biya ne a madadin jihar bisa umurnin Mai Girma Gwamna.
6. Duk da haka, gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta ci gaba da zama mai kishin gaskiya, ingantacciyar tafiyar da kudi, bayyana gaskiya, da rashin yarda da cin hanci da rashawa, ba tare da ta yarda mutuncin jami’anta ya zube a hannun makirci na siyasa daga wasu marasa kishin kasa ba.
7. Gwamnati na nanata cewa ba ta da wata shakka a kan gaskiya da amincin Darakta Janar na Sashen Kula da Baki Hon. Abdullahi Ibrahim Rogo.
8. Muhimmin abu, gwamnatin NNPP za ta ci gaba da bude kofa ga suka bisa gaskiya da doka, amma ba za ta lamunci makircin siyasa ta hanyar yada ƙarya don bata sunan gwamnati ba.
9. Gwamnatin Kano na sane da ayyukan wani bangaren adawa da ke Æ™oÆ™arin tarwatsa mulkin yanzu ta hanyar yada irin waÉ—annan labarai a kafafen sada zumunta don yaudaran jama’a.
10. A lokacin tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje, wannan sashin ne ya kashe sama da Naira biliyan 20 a cikin watanni uku kacal tsakanin Fabrairu zuwa Mayu 2023 bayan APC ta sha mummunan kaye a hannun NNPP.
11. Tsawon shekaru takwas na mulkin da ta gabata, an yi fama da cin hanci da rashawa tare da asusun ɓoye-ɓoye na tsohuwar Uwar Gida da kuma sayen gidaje a Dubai da Saudiyya.
12. Jama’ar Kano ba su manta da bidiyon cin hanci na daloli da ya shafi tsohon Gwamna Ganduje ba.
13. A lokacin gwamnatin da ta gabata, kwace Æ™asa da dukiyar jama’a ya zama ruwan dare ga iyalan masu daraja ta farko da mukarrabansu.
14. Gwamnati na sane cewa jam’iyyar adawa ta buÉ—e ofishi musamman don rubuta Æ™orafe-Æ™orafe da nufin bata jami’an gwamnati mai ci yanzu da hana su tallafa wa Gwamna wajen gina Kano mai albarka.
15. A cikin shekaru biyu da suka gabata na wannan gwamnati, masu zuba jari daga ciki da wajen Æ™asar nan sun fara nuna sha’awa sosai a Kano saboda gaskiya da rikon amana.
16. Jama’ar Kano da ma al’ummar Najeriya na yabawa gwamnatin Kwankwasiyya-Gida-Gida saboda gaskiya cikin tafiyar da gwamnati, wanda ya sa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya zama daya daga cikin gwamnonin da suka fi samun yabo a tarihin Mulkin jamhuriyyar Dimokradiyya ta hudu.
17. Wannan ya tabbata ne ta hanyar lambobin yabo da dama da ake ta ba shi daga gida da waje.
18. Gwamnati za ta ci gaba da girmama kafafen watsa labarai, amma ga waÉ—anda ke aiki bisa gaskiya da ka’idojin aikin jarida, ba waÉ—anda ke bari a yi amfani da su wajen yaudarar jama’a da Æ™arya ba.
19. Domin fayyacewa, Sashen Kula da Baki a kowace gwamnati aiki ne na gudanarwa kawai. Abinda aka dora masa shi ne tsara tarukan gwamnati, karɓar baki, shirya bukukuwa da jigila, da kuma kula da wasu buƙatu na musamman. Ba ya da ikon kashe kuɗi kai tsaye sai bisa tsarin gwamnati da amincewa bisa tsarin kasafi.
20. Saboda haka, zargin da ake yadawa ba komai ba ne illa tatsuniya da aka tsara da gangan don siyasa da neman tasiri a zaben 2027.
21. Jama’a su sani cewa gwamnatin Kano ba ta da abin boyewa . Kowanne jami’in gwamnati, ciki har da Darakta Janar na Protocol, na shirye ya bada cikakken bayani ga hukumomin yaÆ™i da cin hanci idan bukatar hakan ta taso.
22. Don haka, jama’ar Kano su fahimci wannan makirci a matsayin shiri na adawa don bata gwamnati da dakile shirye-shiryen raya jihar. Amma wannan Æ™arya ba za ta yi nasara ba
23. Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kuduri aniyar ci gaba da tafiyar da gwamnati cikin gaskiya da adalci, kuma ba za ta lamunci ƙaryar siyasa ko propaganda su rushe wannan himma ba.
24. Wannan gwamnati ta Kano ta gargadi masu adawa da su daina yada Æ™arya, in ba haka ba za ta É—auki matakan shari’a a kansu.
25. Domin shari’ar tana gaban kotu mai hurumin sauraron irin wannan al’amari, gwamnatin Kano za ta bar kotu ta yi aikinta har sai lokacin da shari’ar ta kammala.