Mazauna Garin Gadama a Kano sunce idan suka binne Gawa sai sunyi kwana 3 suna gadin mamaci don kada a sace sassan jikinsa
Daga Maryam Gadon Kaya
Al'ummar garin Gadama da ke ƙaramar hukumar Kumbotso a Kano, sun nemi ɗaukin mahukunta kan yadda maƙabartun yankinsu suka cika al'amarin da ya sanya a duk lokacin da aka yi musu rasuwa suke shiga cikin damuwa kan rashin wurin da za su binne ƴan uwansu,
Baya ga barazanar tsaro da suke fuskanta a tsofaffin maƙabartun nasu a yankunan nasu.
Wasu daga cikin mazauna yankin sun shaidawa manema labarai cewar, biyo bayan yadda maƙabartun nasu suka cika yanzu haka sun haɗa aƙalla Kuɗi sama da Miliyan Shida 6 da nufin sayen wasu gonaki da kuɗinsu suka tasamma miliyan 40,
Domin cigaba da binne Æ´an uwansu idan sun rasu, amma sauran kuÉ—in sun gagaresu haÉ—awa don haka suke kira da a kai musu É—auki.
Domin kawo karshen wannan tashin hankali da furgicin da suke ciki babu dare babu rana.