Ƙaiƙayi ne babban dalilin da ke hana mata sanya rigar-mama
Daga Hafsat Muhammad Abuja
Wasu mata a Najeriya sun bayyana cewa dalilan da suka sa ba su fiye saka rigar-mama ba da su ka haɗa da rashin sakewa, lafiyar fata da kuma ganin dama.
Binciken jaridar PUNCH Healthwise ta yi ya gano cewa da yawa daga cikin matan sun ce ƙaiƙayi shine babban dalilin da ya sanya su ke kin saka rigar-mama saboda tana haddasa musu matsalar fata, matsewa da rashin walwala, yayin da wasu suka danganta hakan da sauyin salon rayuwa.
Wasu matan sun shaidawa Punch cewa sun fi sakewa ma da jin dadin jikin su, gami da jin cewa sun cika cikakkun mata a idon tsaran su mata idan su ka fita ba tare da rigar-mama ba.
Glory Joseph, wata mata mai shekara 28, ta ce girman mamanta ne ya sanya ta ajiye amfani da rigar-mama saboda da matsarta da ta ke yi, inda hakan ke haifar mata da radadi da takura.
Haka nan, Oladele Omowunmi ta ce ƙarfen rigar-mama ya dinga damunta har sai da ta daina gaba ɗaya.
Sauran mata da suka hada da Abigail Oluchi, Oluwatosin Abayomi da Hussain Adenike sun bayyana cewa jin kwanciyar hankali, kwarin gwiwa, da shawarar likita sun taimaka musu wajen yanke wannan hukunci, duk da kallon da mutane ke musu a waje.
Sai dai masana sun gargadi cewa duk da amfanin rigar nono wajen daidaita jiki, rage ciwon baya, hana faduwar nono da ƙara kwarin gwiwa, amfani da wacce bata dace ba kan jawo matsalar fata, kamuwa da cuta.
Sun shawarci mata da su fifita samun rigar da ta dace da jikinsu, tsafta da kuma kayan da suka fi dacewa domin guje wa barazanar lafiya.