Jami'an NDLEA da na ƴansanda sun kama mutune 57 bisa zargin zargi da ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a Kano
Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta jihar Kano tare da haɗin gwiwar ‘yansanda sun kama mutune 57 da ake zargi da laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi a wani samame na haɗin gwiwa a fadin jihar.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta NDLEA a Kano, Malam Sadiq Muhammad-Maigatari, ya fitar a ranar Lahadi a Kano.
Sanarwar ta bayyana cewa an gudanar da wannan aiki a ranakun 24, 25 da 27 ga watan Satumba a matsayin wani ɓangare na ci gaba da kokarin Kwamitin Hadin Gwiwa na Kano kan Maido da Zaman Lafiya da kuma Farfado da Matasa, ƙarƙashin jagorancin Yusuf Kofar Mata domin kawar da laifi a jihar.
An gudanar da samamen a yankuna irin su Kofar Ruwa da Tashar Rami da Rijiyar Lemo da Kurna da Mil Tara da Zage da Dorayi Karshen Waya da Dawanau da Filin Idi waɗanda aka gano a matsayin cibiyoyin harkar miyagun ƙwayoyi.
“Jami’ai sun kwato nau’o’in miyagun ƙwayoyi daban-daban da kuma makamai na gargajiya da dama, yayin da binciken farko ke ci gaba domin gurfanar da waɗanda aka samu da laifi a gaban kotu,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta rawaito Yusuf Kofar Mata yana tabbatar da kudirin kwamitin wajen kawar da matsalar shan miyagun ƙwayoyi da laifukan da suka shafi ta’addanci a Kano.
Ya yabawa jami’an NDLEA da ‘yan sanda bisa sadaukar da kansu, tare da yin kira ga shugabannin al’umma, iyaye da ƙungiyoyin fararen hula da su tallafa wa yaƙin da ake yi kan miyagun ƙwayoyi da ta’addanci.
Haka kuma, kwamandan NDLEA a Kano, Abubakar Ahmad, ya gode wa Gwamna Abba Kabir-Yusuf bisa goyon bayansa.
Ya ce jajircewar gwamnatin jihar wajen dakile shan miyagun ƙwayoyi da ‘yan daba ya ƙarfafa matuƙa shirye-shiryen tsaro da farfado da matasa da ake gudanarwa a yanzu.