Mai martaba Sarkin Kano, Khalifa Malam Muhammadu Sanusi II, ya ce Najeriya ta daɗe tana fama da shugabanni waɗanda ba su da nagarta.
Ya bayyana haka ne a bikin “Kano International Poetry Festival” da aka yi a Kano a ranar Asabar, inda ya ce matsalolin ƙasar nan sun samo asali ne daga rashin shugabanci na gari, kamar yadda Aminiya ta rawaito.
“Kowace rana kuna gani a jaridu da labarai, ’yan majalisa suna ɓata lokaci kan abubuwan da ba su da amfani, yayin da sauran ƙasashe suke tattauna abubuwa kamar sauyin yanayi da fasahar zamani,”in ji shi.
Ya ƙara da cewar: “Amma mu har yanzu muna ta gardamar kan ƙabilanci da addini kamar yadda aka yi tun a shekarun 1960,” in ji shi.
Sanusi ya roki matasa da su tashi tsaye su ɗauki ragamar shugabanci daga hannun tsofaffin da suka daɗe suna riƙe da mulki.
Ya kuma kare da maganar cire tallafin man fetur, inda ya ce Najeriya da ta ci gaba da biyan tallafin da tuni ƙasar ta yi rauni.
Ya bayyana cewa tallafin man bai amfanar da Najeriya ba, face ƙara bunƙasa masana’antun ƙasashen waje maimakon a gyara na cikin gida.
“Da biliyoyin da aka kashe wajen biyan tallafi da su aka saka a gyaran matatun mai tun 2012, da yanzu Najeriya ta fi haka,” in ji shi.
Sanusi ya kuma yi gargaɗin cewa yawan karɓo bashi da kuma ɓatar da shi da gwamnati ke yi zai iya jefa tattalin arziƙin Najeriya cikin mawuyacin hali a nan gaba.