NNPP ta nesanta kanta da shirin Kwankwaso na komawa APC
Sakataren jam’iyyar NNPP na Æ™asa, Dr. Ogini Olaposi, ya bayyana cewa shirin komawa jam’iyyar APC ba na jam’iyyar NNPP ba ne, sai dai na Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Æ™ungiyar Kwankwasiyya.
Ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Legas, bayan da Kwankwaso, tsohon gwamnan Jihar Kano kuma É—an takarar shugaban Æ™asa na NNPP a 2023, ya sanar a karshen mako cewa shi da magoya bayansa sun shirya shiga jam’iyyar APC mai mulki.
Olaposi ya ce wannan mataki ya tabbatar da cewa Kwankwaso da Æ™ungiyarsa ba su cikin jam’iyyar NNPP tun bayan da aka kore su saboda zargin aikata ayyukan cin amanar jam’iyya.
Ya kara da cewa duk wani tattaunawa da za a yi da Kwankwaso daga yanzu za ta kasance a matsayin nasa mutum É—aya, ba a madadin jam’iyyar ba.
Ya bayyana cewa NNPP za ta ci gaba da tsara tsarin cikin gida domin shiryawa zaben 2027, bayan rikici da shari’o’in da magoya bayan Kwankwaso suka haddasa.
A cewar Olaposi, yarjejeniyar haÉ—in gwiwa tsakanin NNPP da Kwankwasiyya ta Æ™are ne bayan zaÉ“en 2023, inda daga baya Kwankwaso ya fara yunÆ™urin kwace jam’iyyar.
Ya ce yawancin magoya bayan Kwankwaso a Kano sun riga sun shiga APC tun da dadewa, kuma yanzu babu jam’iyyar siyasa da yake da ita. Olaposi ya jaddada cewa duk wata tattaunawa da Kwankwaso ke yi, hakki ne nasa a matsayin É—an Æ™asa, amma ba a madadin NNPP ba, domin a hukumance har yanzu an kore shi daga jam’iyyar.