Sanata Kawu Sumaila ya yi Maraba da matakin Gwamnatin Kano na bawa kananan hukumomi ƴancin Kai gashin kai
Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Sanata Suleiman Abdurrahman Kawu Sumaila, OFR, PhD, ya bayyana jin daɗinsa kan matakin da gwamnatin Kano ta ɗauka na aikawa da kudirin ba wa kananan hukumomi 44 cikakkiyar ‘yancin kuɗi da gudanarwa zuwa ga Majalisar dokokin jihar.
Sanata Kawu ya ce wannan ci gaba ya tabbatar da sahihancin fafutikar da ya fara a majalisar dattawa a ranar 15 ga Mayu, 2024, inda ya gabatar da muhimmin kuduri na dawo da ‘yancin kananan hukumomi, wanda daga baya kotu ta tabbatar a lokacin shugabancin Bola Ahmed Tinubu.
A zaman majalisar zartarwar Gwamnatin Kano karo 31 da aka gudanar a masaukin gwamnati na Kwankwasiyya City, Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya amince da kudirin, wanda zai tafi majalisar dokoki ta jiha don amincewa.
Sanata Kawu ya ce: “Wannan nasara ce ga dimokuraɗiyya da al’ummar Najeriya. Abin da muka fara a majalisar dattawa, kotu ta tabbatar, yanzu kuma jihar Kano ta rungume shi. Na ji daɗin ganin wannan ya zama tarihi.”
Ya kuma jaddada aniyarsa na ci gaba da kare dimokuraɗiyya da inganta mulki a ƙasar nan.