Rundunar Æ´an sandan Jihar Kano ta cafke wani mutum da ake zargi da satar mota tare da gano wata mota da aka gano da shubuha a mallakarta.
Kakakin rundunar Æ´an sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, 13 ga Satumba, 2025.
Ya ce, a unguwar Sharada, wani mutum mai suna Abubakar Yakubu ya karɓi motar Mercedes-Benz daga wata mata da zummar gyaran AC, amma ya gudu da ita ya kuma sayar, inda daga baya aka gano shi da wata motar Toyota Corolla da ya saya a Kaduna.
Rundunar ta cafke shi, ana kuma ƙoƙarin gano Mercedes ɗin.
Haka kuma, wani mutum daga unguwar Mariri ya shiga hannun Æ´an sanda bayan ya sayi mota da kuÉ—i sama da naira miliyan biyu, daga baya aka samu shakku kan sahihancin mallakar motar.
Rundunar ta kwace motar, kuma ana ci gaba da bincike.
Kwamishinan Æ´an sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da gurfanar da masu aikata laifi a kotu.