Yadda aka tsinci Gawar wani Mutum a karkashin gadar Jirgin Kasa Jihar Kano
An tsinci gawar wani mutum a hayen ƴan Kaba, kusa da Tokish School a ƙaramar hukumar Nasarawa a Jihar Kano.
Shaidun gani da ido sun ce an gano gawar ne a ƙarƙashin wata gada da ke daura da titin jirgin ƙasa.
Ana kyautata zaton cewa ruwa ne ya yi awon gaba da mutumin sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka tafka a yankin.
Har yanzu ba a gano dangin mamacin ba, kuma saboda yanayin jikinsa, al’umma suka yi masa jana’iza a wajen da abin ya faru.