Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC) ta sake jaddada aniyarta ta kare masu amfani da harkokin sadarwa tare da ƙarfafa tsaron hanyoyin sadarwa, ta hanyar aiwatar da tsarin tantance na'urorin sadarwa mai suna NCC Device Checker Platform.
Hukumar ta bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ta gudanar a ofishinta na shiyya a ranar Alhamis, 29 ga Oktoba, 2026, domin wayar da kan jama'a da ƙarfafa bin ƙa'idojin fasaha da na amincewa da na'urorin sadarwa a Najeriya.
A cewar hukumar, tsarin Device Checker yana bai wa masu amfani da na'urori da sauran masu ruwa da tsaki damar tantance matsayin amincewar na'urorin da ke amfani da katin SIM. Wannan zai taimaka wajen magance yaɗuwar na'urorin jabu, na'urorin da aka yi musu kwafi ba bisa ƙa'ida ba, da waɗanda ba su cika ƙa'idoji ko ba su da izinin amfani da su ba.
NCC ta bayyana cewa ta sauƙaƙa hanyoyin samun lasisi da daidaita harkokin kasuwancin na'urorin sadarwa, matakin da ya ba da damar samun lasisi ga adadi mai yawa na dillalan na'urori a Jihar Kano.
Haka kuma, hukumar ta gudanar da tarukan wayar da kan masu shigo da na'urori daga ƙasashen waje da sauran masu ruwa da tsaki a Legas da wasu sassan ƙasar, domin ƙara fahimtar ƙa'idojin da suka shafi amincewa da na'urorin sadarwa.
Domin sauƙaƙa bin waɗannan ƙa'idoji, NCC ta samar da manhajar Device Checker mai sauƙin amfani, wadda ke ba wa masu ruwa da tsaki da aka ba izini damar bincika lambar IMEI ta na'ura tare da aika bayanan da suka dace kai tsaye zuwa tsarin.
Hukumar ta kuma shawarci masu amfani da na'urori da su tantance matsayin na'urar kafin saye ta hanyar ziyartar shafinta na intanet: www.ncc.gov.ng/devicechecker.
An kuma shawarci masana'antun na'urori, masu shigo da su, masu rarrabawa da dillalai da su karanta jagorar Type Approval and Device Verification Guide ta www.ncc.gov.ng/DeviceCheckerGuide, domin fahimtar nauyin da ke kansu da kuma tabbatar da bin ƙa'idojin hukumar.
NCC ta ƙara fayyace cewa tsarin Device Checker ba na sa ido kan sirrin mutane ba ne. Hukumar ta ce tsarin ba ya shiga ko karanta bayanan sirri, saƙonni, hotuna, lambobin waya, bayanan kuɗi ko wasu abubuwan sirri da aka adana a cikin na'ura.
A cewar hukumar, aikin tsarin ya taƙaita ne ga tantance na'ura da tabbatar da bin ƙa'idojin da suka shafi amfani da ita.
Masu buƙatar ƙarin bayani, kai ƙorafi ko neman taimako za su iya tuntuɓar hukumar ta hanyar 315 Consumer Toll-Free Number, wato lambar kira kyauta ta masu amfani da harkokin sadarwa.
Hukumar ta buƙaci jama'a da su riƙa sayen na'urori daga amintattun dillalai masu lasisi, su tabbatar da matsayin na'ura kafin saye, sannan su yi amfani da hanyoyin intanet da hukumar ta tanada domin yanke shawarar saye cikin sani.
Haka kuma, ta yi kira ga masana'antun na'urori, masu shigo da su, masu rarrabawa da dillalai da su tabbatar da cikakken bin ƙa'idojin amincewa da na'urorin sadarwa.
A ƙarshe, NCC ta jaddada aniyarta ta kare masu amfani da sadarwa, inganta gasa ta gaskiya, ƙarfafa tsaron hanyoyin sadarwa da samar da ingantaccen tsarin sadarwa da jama'a za su amince da shi a Najeriya.
Hukumar ta kuma yaba da rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen wayar da kan jama'a game da wannan shiri.
