Nan bada jimawa ba za ku yi murnar manufofin Shugaba Tinubu - Abba Gida-Gida
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya buÆ™aci ’yan Najeriya su yi haÆ™uri da manufofin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa nan ba da jimawa ba al’umma za su fara amfana da sauye-sauyen tattalin arziÆ™in da gwamnatin ke aiwatarwa.
Gwamnan, wanda babban jami’in jam’iyyar APC na Æ™asa, Muhammad Jamo Yusuf, ya wakilta, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin Æ™addamar da kwamitin yaÆ™in neman zaÉ“en APC na Æ™aramar hukumar Tarauni, domin zaÉ“en 2027, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce gwamnatin Tinubu ta ɗauki matakai masu wahala amma sun zama wajibi ne domin daidaita tattalin arziƙin ƙasar.
Abba Yusuf ya ce darajar naira ta samu daidaito, lamarin da ya taimaka wajen samar da yanayin da 'yan kasuwa da masu zuba jari za su iya gudanar da harkokinsu cikin sauƙi.
Ya buÆ™aci ’yan Najeriya su ci gaba da haÆ™uri, yana mai cewa a Æ™arshe za su yi murnar sakamakon manufofin gwamnatin.