Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya tabbatar wa manema labarai afkuwar haka, inda ya ce lamarin ya faru ne da safiyar yau Juma’a.
Ya ce an yi awon gaba da tsohon mataimakin gwamnan ne lokacin da ƴan bindigar suka kutsa cikin gidansa da ke ƙauyen Gwagi a karamar hukumar Wamba na jihar.
Mai magana da yawun ƴan sandan ya ce haɗin gwiwar ƴan sanda da wasu jami’an tsaro suna can suna ci gaba da bin sawun maharan da nufin ceto wanda aka yi garkuwa da shi.