Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, LP, Peter Obi a jiya Alhamis, ya bayar da gudummawar Naira miliyan 10 ga jami’ar Paul da ke Awka a Anambra.
Obi ya nanata matsayarsa cewa, ingantaccen ilimi da kiwon lafiya na da matukar muhimmanci ga ci gaban kowace kasa.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara jami’ar da ke Awka.
Ya ce ziyarar tasa za ta zo ne a karshen shekarar 2022, lokacin da ya samu gayyatar amma ya jinkirta zuwa bayan zabe saboda ba ya son mutane su dora mata ma'anar siyasa ko yakin neman zabe.
Tsohon gwamnan na Anambra ya ce ya kasance a kullum yana ziyartar cibiyoyin jinya uku da makarantun sakandare uku duk wata domin tallafa musu a matsayinsa na dan kasa mai zaman kansa.