Kakakin rundunar yansandan jihar Ondo, SP Olufunmilayo Odunlami Omisanya, ta tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin.
Omisanya ta ce haɗarin ya hada da wata mota da babur ɗin acaɓa.
“Akwai haÉ—arin da ya yi sanadin mutuwar wani direban babur, kuma maimakon mutanen da ke kusa da su su taimaka su ceci waÉ—anda haÉ—arin ya shafa, sai suka yi kan direban ta hanyar kashe matashin tare da kona motarsa,” inji ta.
Kakakin Æ´ansandan ta ci gaba da cewa, amma da gaggawar zuwa sa Æ´ansandan suka yi, da an kashe iyayen direban su ma.
Ta ce iyayen ba sa cikin motar da dan nasu ke tukawa, amma sun zo wurin ne kawai don ganin abin da ke faruwa.
“A gaba É—aya, an tabbatar da mutuwar mutane biyu yayin da wasu shidan da suka samu raunuka a hatsarin a halin yanzu suna samun kulawa a asibiti,” in ji PPRO.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya tattaro cewa ana zargin direban cewa dan damfara ta intanet ne, wanda aka fi sani da ‘Yahoo boy’.