A yau Laraba ne wata kotu a Jos ta yankewa wani mutum, Timzing Marchap hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari bisa samunsa da laifin mallakar wata karamar bindigar da ba ta da lasisi.
Alkalin kotun, Thomas Ajitse, ya yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin ne bayan ya amsa laifinsa.
Sai dai kuma Ajitse, ya ba shi zabin biyan tarar Naira dubu 100,000.
Tun da fari, mai gabatar da kara, Insp. Ibrahim Gokwat, ya shaidawa kotun cewa a ranar 15 ga watan Fabrairu, an kama wanda ake zargin a Kogin Nasa da ke karamar hukumar Wase a jihar tare da wata bindiga, kirar gida mara lasisi.
Ya ce wanda ake tuhumar ya kasa bayar da gamsasshen bayani ba kan dalilin da ya sa ya mallaki wannan bindigar kirar gida da ba ta da lasisi .
Gokwat ya kara da cewa a yayin binciken ‘yan sanda ya amsa laifin aikata laifin.
Dan sanda mai shigar da kara ya ce laifin ya saba wa dokar rike makami ta ƙasa.