Hukumar Hisbah a Kano sun kama wanda ake zargi da safarar mata
Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta ce ta gano wasu Mata da ake zargin ana ƙoƙarin yin safararsu zuwa wasu ƙasashe domin neman kuɗi.
Mataimakin babban Kwamandan hukumar Dakta Mujahiddin Aminuddeen, ne ya bayyana hakan.
Dakta Mujahiddin ya ce, hukumar ta É—auki matakin gaggawa domin hana aukuwar lamarin tare da tabbatar da cewa, an tsare lafiyarsu, domin kariya daga fadawa cikin haÉ—arin cin zarafi ko bautar da su.