Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya bayyana cewa Majalisar ta 10 da Majalisar Dattawa gaba ɗaya suna goyon bayan shirin ciyo bashi na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Yayin taron shekara-shekara karo na 8 na African Network of Parliamentary Budget Offices (AN-PBO) a Abuja ranar Litinin, Abbas ya karyata rahotannin da ke cewa Majalisar ta ƙi amincewa da shirin, yana mai kiran rahotannin na ƙarya ne.”
Ya ce Najeriya, kamar kowace ƙasa mai cigaba, na buƙatar jingina da lamuni domin gina ababen more rayuwa, farfaɗo da tattalin arziki, da kare marasa zaman galihu.
Abbas ya tabbatar cewa bashin da ake ciyowa za a karkatar da shi ne zuwa manyan ayyukan ci gaba kamar wutar lantarki, sufuri, da noma, ba don ci da sha ba.
Kakakin ya kuma jaddada cewa Majalisar ta kafa Ofishin Nazari da Tsare-tsaren Kasafin Kuɗi domin bayar da sahihin bayani kan lamuni da dorewar tattalin arziki.
Ya ce duk da muhimmancin bashi, hana asarar kuɗaɗe ta hanyar cin hanci na da matuƙar muhimmanci, inda ya bayyana cewa Najeriya na asarar kusan dala biliyan 18 duk shekara.