Fursunoni 68 sun samu nasara a jarrabawar NECO a Kano
Fursunoni 68 a Jihar Kano ne suka ci jarabawar kammala sakandaire ta NECO ta shekarar 2025, a cewar hukumar kula da fursunoni ta Najeriya, reshen jihar.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, fursunonin sun ce wannan nasarar ta kasance abin farin ciki gare su inda suka bayyana cewa hakan zai zama wata babbar dama wajen sauya rayuwarsu gaba É—aya.
Hukumar ta bayyana cewa wannan nasara ta samu ne sakamakon tallafin gwamnatin Kano, wadda ta É—auki nauyin ci gaban ilimin fursunonin.
"Wannan shiri ya yi daidai da dokar hukumar kula da fursunoni ta Najeriya ta 2019, wadda ke mai da hankali kan gyara da sake tarbiyyar fursunoni ta hanyar ilimi da horo na sana’o’i." in ji sanarwar.
Gwamnatin Jihar Kano ta Æ™ara jaddada aniyyarta ta samar da damammakin ilimi ga fursunoni domin Æ™arfafa su su zama abin koyi nagari a cikin al’umma.
Wannan mataki na cikin shirin muradun shugaba Tinubu na 'Renewed Hope', wanda hukumomin Æ™asar suka ce yana Æ™unshe da inganta rayuwar duk ‘yan Najeriya cikin har da fursunoni.