Onanuga ga El-Eufai: Kwantar da hankalin ka, Tinubu ba zai tafi da kujerar mulki gida ba idan ya sauka daga mulki a 2031
Fadar Shugaban Ƙasa ta mayar da martani ga tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, wanda ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da yunkurin zama shugaban ƙasa na dindindin.
A wata ganawa da ya yi da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar a karshen mako, El-Rufai ya bayyana cewa alamu sun nuna cewa Shugaba Tinubu na shirin komawa kamar Paul Biya na Kamaru wanda ke kan kujerar mulki tun 1982.
Ya ce duk wasu shaida da ke nuna cewa shugaban Æ™asa mai bin dimokuraÉ—iyya ne, “Æ™arya” ce kawai, domin gwamnatin yanzu tana kaucewa hanya tana karkata zuwa mulkin kama-karya.
Sai dai a cikin martanin da ya fito daga mai baiwa shugaban Æ™asa shawara kan harkokin bayani da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya ce: “Shugaba Tinubu É—an dimokuraÉ—iyya ne wanda bai da niyyar ci gaba da mulki bayan 28 ga Mayu, 2031, idan ya sake lashe zabe a 2027.”
Onanuga, wanda ya nuna cewa El-Eufai , wanda shi ne jagoran jam’iyyar ADC na bukatar taimako, ya ce tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), ya fahimci cewa yunkurin da abokan tafiyarsa a sabuwar jam’iyyarsa ke yi na hana Tinubu sake samun nasara a 2027, ba zai yi nasara ba.
Ya Æ™ara da cewa: “Wannan makirci ba zai kai ga nasara ba; aikin da ya riga ya zama tamkar mafarki marar mafita.”