DSS sun gayyaci Abubakar Malami SAN kan harin da aka kai masa a Jihar Kebbi
Tsohon Ministan Shari’a na Æ™asa, Abubakar Malami (SAN), ya tabbatar da cewa Hukumar Tsaro ta DSS ta gayyace shi domin bayar da bayani kan harin da aka kai masa da tawagarsa a Jihar Kebbi ranar 1 ga Satumba, 2025.
Malami ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litini
Ya ce korafin da ya haifar da binciken na da nasaba da abokan hamayyar siyasarsa a jihar.
Ya yaba wa DSS bisa yadda suke gudanar da binciken cikin gaskiya da adalci, yana mai cewa an kula da shi da mutuntawa.
Ya kuma jaddada aniyarsa ta ci gaba da bada hadin kai har sai an kammala binciken.