Najeriya ta cimma kashi 96 cikin 100 na adadin Gangar Mai da Kungiyar OPEC ta bata
Hukumar Kula da albarkatun Man Fetur a tsandauri ta bayyana cewa an samu ƙaruwa a fitar da danyen mai da iskar gas a watan Agusta 2025, inda aka samu matsakaicin fitarwa na ganga miliyan 1.63 a kowace rana, wanda ya karu daga ganga miliyan 1.58 a watan Agusta na shekarar da ta gabata.
Sanarwar kakakin hukumar Eniola Akinkuotu ce ta tabbatar da haka, inda ta ce bayanan sun nuna an samu karuwar kashi 5.47 cikin É—ari idan aka kwatanta da watan Agusta na bara, wanda aka fitar da ganga miliyan 1.36 a rana.
A watan Agustan Nigeria ta cimma kashi 96 cikin ɗari na adadin da ƙungiyar OPEC ta ware mata, wanda aka samu ganga miliyan 1.5 a kowace rana.