Jami'an Tsaron Najeriya 53 ne suka rasa ransu cikin Makonni 2
AÆ™alla jami’an tsaro 53 ciki har da sojoji, Æ´an sanda, jami’an NSCDC, kwastam, da na shige da fice da Æ´an sa kai, aka kashe a sassa daban daban na Najeriya cikin makonni biyu da suka gabata.
Yawancinsu Æ´an bindiga ne suka halaka su yayin hare hare, wasu kuma a wuraren binciken tsaro.
Rahotanni sun nuna cewa daga Janairun 2023 zuwa Oktoban 2024 an kashe jami’an ’yan sanda 229 a faÉ—in Æ™asar.
Masu kisan sun haɗa da ƴan bindiga, Boko Haram, IPOB, da ƴan fashi da kuma ƙungiyoyin asiri.
Sabbin hare haren sun fi kamari a jihohin Benue da Kogi, inda aka kashe jami’an tsaro da dama tare da sace wasu.
Sai dai hukumar DSS ta gurfanar da mutane tara a Abuja kan zargin kisan gilla, fataucin makamai da kai hare hare a Benue da Filato.