Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya ce bai damu da shan kayen da ya sha a zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Ortom wanda ya tsaya takarar Sanatan Benue ta Arewa, sannan ya sha kaye a hannun dan takarar jam’iyyar APC, ya bayyana haka ne a wajen kaddamar da makarantar sakandiren gwamnati da ke Kpor a karamar hukumar Gokana.
A cewar wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Nathaniel Ikyur ya fitar, gwamnan ya jaddada cewa zai ci gaba da bayar da shawarwarin tabbatar da gaskiya da adalci.
Ya ce: “Ban sha kashe ba kuma na tsaya tsayin daka, sannan ina alfahari da haduwa da Gwamna Nyesome Wike da wasu da dama da suka zabi tsayawa kan gaskiya da tabbatar da adalci, gaskiya da adalci ga kasar nan.
“Muna da duk abin da muke bukata a Najeriya, abin da ya rage shi ne adalci, adalci da adalci, kuma ina alfahari da cewa tun da farko na tsaya tsayin daka na ce bayan shekaru takwas na shugabancin Arewa, sai a kara shekaru takwas zuwa Kudu, kuma ina farin ciki da cewa yau ga inda muke.”
Gwamnan ya kuma yabawa al’ummar jihar Rivers bisa goyon bayan gwamnansu, Nyesom Wike, tare da mara masa baya a duk wani buri nasa, inda ya bayyana shi a matsayin “babban dan Najeriya, mai kishin kasa, mutum mai imani da adalci, gaskiya da adalci.”