An yaba wa wani matuƙin jirgin ɗan Afirka ta Kudu kan nasarar saukar gaggawa da ya yi, bayan da ya lura da wani maciji nau'in gamsheƙa a ƙarƙashin kujerar zamansa.
Rudolph Erasmus ya ɗauko fasinjoji huɗu daga birnin Cape Town zuwa arewacin Nelspruit da safiyar ranar Litinin amma saboda artabun da ya yi da gamsheƙar ya sa shi saukar gaggawa, kamar yadda kafofin yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito
Direban ya shaida wa kafar yaÉ—a labarai ta Time Live cewa “ina duba Æ™arÆ™ashin kujerata, kawai sai na ga macijin na Æ™oÆ™arin mayar da kansa Æ™arÆ™ashin kujerar”.
Sarar gamsheka zai iya kashe mutum cikin mintuna 30 idan ba a É—auki matakan da suka dace ba.
Minista harkokin sufurin jiragen sama ta Afirka ta kudu ya yaba da jarumtar Mr Eramus, kamar yadda shafin yanar gizo na news24 ya ruwaito.
Direban jirgin yace ya shiga yanayi mai rikitarwa wajen fada wa fasinjojin ainihin abin da ya sa ya yi saukar gaggawar.
“Na fada musu cewa akwai matsala., akwai maciji a cikin jirgin. Ina da yaÆ™inin cewa yana Æ™arÆ™ashin kujera ta don haka za mu yi saukar gaggawa”.
Ya yi ƙoƙarin ganin ya yi saukar gaggawa a birnin Welkom dake Afirka da Kudu.
Injiniyoyin da suka caje jirgin ba su ga gamsheƙar ba, inji Mr Eramus.
Ya ce yana sa ran komawa bakin aikinsa a ranar Laraba.
BBC Hausa