Wata majiya mai ƙarfi ta tsaiguntawa Jaridar Raihana cewa Alasan Ado Doguwa ya shirya tsaf domin siyan ƙuri'un akwatunan da za'a sake zabukan su a ƙananun hukumomin Doguwa da Tudun Wada domin samun damar lashe zaben da za'ayi na ranar Asabar 15/04/2023. Hakan na nuni da cewa akwai yiwuwar Alasan ya koma kujerar sa domin babu wani Talaka da zai ga wannan kyautar ta mashin ya tsallake bai karba ba.
Tambayar a nan itace shin jami'an tsaro sun shirya ƙwace ko hana bada cin hanci don yin zabe a filin zabe.